Bangaren kasa da kasa: Za a fara gudanar da wani taron kara wa juna ilimi kan rayuwar zamantakewar al'umma a mahangar kur'ani mai tsarki a birnin London na kasar Birtaniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na bangaren hulda da jama'a na cibiyar harkokin addinin musulunci ta kasar Birtaniya cewa; Za a fara gudanar da wani taron kara wa juna ilimi kan rayuwar zamantakewar al'umma a mahangar kur'ani mai tsarki a birnin London na kasar Birtaniya. Bayanin ya ci gaba da cewa a dabra da hakan kuma za a bayar da horo ga masu bukata dangane da yadda kur'ani ya koyar dad an adam kiyaye adalci da tausaya wa maras shi, da kuma tarbiyantar da 'ya 'ya sahihin tafarkin rayuwa ta yadda za su taka rawa wajen shiryar da al'umma a gaba. Malamin jami'ar nan na kasar Birtaniya Ramadan Alausi shi ne zai jagoranci bayar da horon.
405782