IQNA

An Kame Wasu Littafai Na Kiyayya Da Mazhabar Shi'a A Iraki

Bangaren kasa da kasa: 'Yan sandan kasar Iraki sun sun kame wasu tarin littafai da yawansu yah aura kwafi miliyan daya da aka rubuta su domin nuna kyama ga mazhabar shi'a, a loakcin da ake kokarin shiga da su cikin kasar ta iyakokin kasar da kasar Jordan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Iraki cewa; a jiya 'yan sandan kasar Iraki sun sun kame wasu tarin littafai da yawansu yah aura kwafi miliyan daya da aka rubuta su domin nuna kyama ga mazhabar shi'a, a loakcin da ake kokarin shiga da su cikin kasar ta iyakokin kasar da kasar Jordan. Rahoton ya ci gaba da cewa an kame wata babbar motar daukar kaya makare da littafai wadanda aka rubuta domin haddasa rikici tsakanin musulmi shi'a da sunna, domin kuwa littafan suna kafirta shi'a ne tare da jingina karairaki gare su domin kawai a tunzura su su kyamaci 'yan sunna, ta yadda hakan zai iya kawo rikici tsakanin bangarorin biyu. Yanzu hakan 'yan sanda kasar Iraki sun shiga gudanar da bincike kan masu littafan, bayan da aka gano cewa za a nufin lardin Salahuddini ne da su.

405720