IQNA

Zane-Zanen Batunci Ga Addinin Musulunci Alama Ce Ta Jahiltarsa

Bangaren kasa da kasa: Zane-zanen batuncin da aka yi ga manzon Allah SAW a kasashen danmark da ma wasu kasashen nahiyar turai, wata babbar alama ce kan jahilcin ma'abuta zane-zanen da addinin muslunci da kuma koyarwarsa, amma a halin yanzu wasu daga cikin musulmi daga yankin gabas ta tsakiya sun bude shafuka na internet domin mayar da martini kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar saudiyya cewa; shahararren marubucin nan na turai Jan Erik Smilodon ya bayyana cewa; Zane-zanen batuncin da aka yi ga manzon Allah SAW a kasashen danmark da ma wasu kasashen nahiyar turai, wata babbar alama ce kan jahilcin ma'abuta zane-zanen da addinin muslunci da kuma koyarwarsa, amma a halin yanzu wasu daga cikin musulmi daga yankin gabas ta tsakiya sun bude shafuka na internet domin mayar da martini kan hakan. Ya ci gaba da cewa abin takaici ne yadda wasu daga cikin al'ummomin turai suka jahilci addinin musulunci, da a ce sun san koyarwa irin ta addinin musulunci da ba su kyamace shi ba. Ya ce ya zama wajibi a kara karfafa batun tattaunawa tsakanin addinai domin samun fahimtar juna.

405654