IQNA

Himmatuwar Matasa Iraniyawa Zuwa Ga Salla Albarkacin Juyin Islama Ne

Bangaren kur'ani: Himmatuwar matasa Iraniyawa zuwa ga salla daya ne daga cikin abubuwan da juyin juya halin musulunci ya kawo na albarka, domin kuwa a halin yanzu matasa suna gudanar da aikace-aikace a cibiyoyi daban-daban na kula da tsayar da salla.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga limamin juma'ar garin Lozaka sheikh Muhammad asadi cewa; Himmatuwar matasa Iraniyawa zuwa ga salla daya ne daga cikin abubuwan da juyin juya halin musulunci ya kawo na albarka, domin kuwa a halin yanzu matasa suna gudanar da aikace-aikace a cibiyoyi daban-daban na kula da tsayar da salla. Shaihin malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar hudubar juma'a makon da ya shige. Ya ci gaba da cewa idan aka kwatanta lokutan da suka gabata kafin samun nasarar juyin juya halin musulunci a Iran da kuma bayan samun nasar juyin juya halin, za a ga banbanci mai tazara tsakanin tarbiyar matasa a wancan lokacin da kuma yanzu, musamman ma bangaren salla da sauran ibadu, wanda kuma acewarsa hakan wata albarka ce da al'umma suka samu sakamakon juyin juya halin musulunci.


405905