Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: a wani zama da aka yi day a shafi karatun kur'ani Muhammad Rafaati ya nuna fice da kwarewa a wannan fanni kuma wannan ya tabbata ne a gaban makaranta da mahardata fitattu na kasa da kasa kamar Abas Salimi da Said Muhsin Musawi Balade alkalin kasa da kasa kan karatun kur'ani da harda da kuma Mahdi Dagadala masani kan Kur'ani da Ahmad Abul Kasimi makaranci na kasa da kasa da kuma da dama daga cikin masu sha'awar karatun kur'ani.
406288