IQNA

Ana Neman Kuri'ar Zabe Ta Hanyar Wulakanta Kur'ani A Norway

16:31 - May 18, 2009
Lambar Labari: 1780031
Bangaren kasa da kasa: Jam'iyar National party wadda day ace daga cikin jam'iyu masu tsattsauran ra'ayi da wuce gona da iri tsakanin jam'iyun siyasa na kasar Norway, ta mayar da hanyar yin wulakanci ga kur'ani da tozarta musulmi babbar hanyar neman kuri'a a zabukan da za a gudanar a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Laha online cewa; Jam'iyar National party wadda day ace daga cikin jam'iyu masu tsattsauran ra'ayi da wuce gona da iri tsakanin jam'iyun siyasa na kasar Norway, ta mayar da hanyar yin wulakanci ga kur'ani da tozarta musulmi babbar hanyar neman kuri'a a zabukan da za a gudanar a kasar. Jam'iyar ta National party ta sanar da cewa daya daga cikin hanyoyin da za ta yi amfani da su wajen neman kuri'a sun hada da kone alkur'ani mai tsarki a gidan talabijin. Yanzu haka jam'iyar ta kulla wani kwantaragi tare da wata tashar talabijin da ke watsa shirye-shiryenta kan tauraron dan adam dag akasar ta Norway, wadda za ta nuna hotunan kona alkur'ani mai tsarki kai tsaye.

406267


captcha