Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro mai take Qods na kuka palastinu na gwagwarmaya a birnin Adana da ke kudancin kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran IN cewa; An gudanar da wani taro mai take Qods na kuka palastinu na gwagwarmaya a birnin Adana da ke kudancin kasar Turkiya.Rahoton ya ci gaba da cewa an gudanar da taron ne da nufin bayyana halin da masallacin Qods yake ciki da irin hadarin da ke tattare da shirin Haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya na share duk wasu abubuwa masu tsarki da ke birnin wadanda musulmi suke girmamawa, da kuma halin da aka jefa al'ummar palastinu ga baki daya, kama daga mazauna yankunan gabar yamma da kogin Jordan har zuwa mazauna birnin Qods da kewaye, balantana uwa uba mutanen Gaza, wadanda har yanzu suke cikin mawuyacin hali, sakamakon kisan kiyashin da suka fuskanta daga yahudawan sahyuniya a farkon shekarar nan.
406290