Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani taro kan matsayin Imam Amirul muminin Ali (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah SAW a birnin Azmir na kasar Turkiya, wanda jami'ar Dokoz ta kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa tare da hadin gwiwa da kwamitin malamai masu bayar da fatawa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna yanakalto daga kamfanin dillancin labaran YENI na kasar Turkiya cewa; Za a gudanar da wani taro kan matsayin Imam Amirul muminin Ali (AS) da kuma iyalan gidan manzon Allah SAW a birnin Azmir na kasar Turkiya, wanda jami'ar Dokoz ta kasar Turkiya ta dauki nauyin shiryawa tare da hadin gwiwa da kwamitin malamai masu bayar da fatawa a kasar. Daya daga cikin wadanda suka shirya gudanar da taron kuma jami'i a jami'ar Dokoz ya bayyana cewa babbar manufar gudanar da wannan taro ita ce kara fito da matsayin Imam Ali (AS) da iyalan gidan manzon Allah (AS) ta yadda za a kara sanin martabarsu da matsayinsu a cikin addinin musulunci, da kuma sani koyarwarsu da dabi'unsu, wanda da dama daga cikin al'ummar musulmi ba su sani ba.
406328