Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wani zaman taro dangane da mahangar musulunci kan harkokin banki da kuma abubuwan da suka danganci harkokin tattalin arziki, wanda za a gudanar a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Albayan cewa; Za a gudanar da wani zaman taro dangane da mahangar musulunci kan harkokin banki da kuma abubuwan da suka danganci harkokin tattalin arziki, wanda za a gudanar a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Shugaban kwamitin da aka dorawa shiryawa tare da gudanar da wannan taro sheikh Hamad Ahmad Shaibani ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan zaman taro ita ce kara wa juna ilimi kan muhimman batutuwa da suka shafi harkokin banki a mahangar musulunci, da kuma sauran harkokin tattalin arziki, ta yadda kasashen musulmi za su yi amfani da hanyoyin da addininsu ya yarje musu wajen warware da dama daga cikin matsalolin da ake fuskanta na tattalin arziki a duniya. Ya ce masana daga kasashen duniya daban-daban za su halarci zaman taron.
406316