IQNA

Wani Dan Jarida Bapalastine Ya Samu Lambar Yabo Ta Duniya

Bangaren kasa da kasa: Wani dan jarida bapalastine da yake aiki tare da jaridar Demotex ya samu lamabar yabo ta duniya, sakamakon rahotannin da ya rika bayarwa dangane da hakikanin abin da ke faruwa a lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yaki kan al'ummar Gaza.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga gidan talabijin al'aqsa cewa; Wani dan jarida bapalastine Iman Muhammad da yake aiki tare da jaridar Demotex ya samu lamabar yabo ta duniya, sakamakon rahotannin da ya rika bayarwa dangane da hakikanin abin da ke faruwa a lokacin da Isra'ila ta kaddamar da yaki kan al'ummar Gaza. An bai wa Iman Muhammad wannan lambar yabo ne mai suna New Media Award sakamakon namijin kokarin da ya yi a lokacin yakin da Isra'ila ta kaddamar kan fararen hula a Gaza da suna yunkurin murkushe gwagwarmayar palastinawa karkashin Hamas, daga cikin muhimman ayyukan da ya yi a lokacin yakin kuwa hard a dauko hotunan kanan yara da mata da suka yi shahada tare da nuna wa duniya hakikanin abin day a faru na rashin imani da yahudawan sahyuniya suka nuna kan al'ummar Gaza.

406372