IQNA

Al'ummar Musulmi Na Bukatar Saiti Na Sahihin Tunani

Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin 'yan majalisar dokokin falastine daga jam'iyar Tagyir Wal Islah Abu Mosameh ya bayyana cewa rashin samun saitin tunani tare da yin watsi da koyarwar addini shi ne babban ummul haba'isin dukkanin matsalolin da al'ummar musulmi ke fama da su a halin yanzu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran tauhid habar cewa; Daya daga cikin 'yan majalisar dokokin falastine daga jam'iyar Tagyir Wal Islah Abu Mosameh ya bayyana cewa rashin samun saitin tunani tare da yin watsi da koyarwar addini shi ne babban ummul haba'isin dukkanin matsalolin da al'ummar musulmi ke fama da su a halin yanzu. Ya ci gaba da cewa abin da al'ummar palastinu ke gani a halin yanzu ya samo asali ne daga barin sahihin tafarki na koyarwar addini ne tun farko da al'umma ta yi, kuma hanya kadai ta fita daga karkashin zalunci da wulakanci da al'ummar musulumi ke gani a palastinu da ma wasu yankuna a duniya ita ce komawa zuwa ga hakikanin koyarwa irin ta addinin, domin kuwa a cewarsa addinin musulunci addini ne na izza da daukaka, kuma matukar aka bi koyarwarsa za a kai wannan sakamako.

406963