Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin manyan malaman addinin na kasar Masar, ya bayyana cewa an mika shawara ga kasashen musulmi domin kafa wata Hadaka ta kamfanonin kasashen musulmi, da nufin karfafa harkokin tattalin arzikinsu gami da kasuwancinsu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na islam online cewa; : Daya daga cikin manyan malaman addinin na kasar Masar, ya bayyana cewa an mika shawara ga kasashen musulmi domin kafa wata Hadaka ta kamfanonin kasashen musulmi, da nufin karfafa harkokin tattalin arzikinsu gami da kasuwancinsu. Wujdi Ganim ya ce tuni kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi na'am da wannan shawara, bisa la'akari da raunin tattalin arzikin wasu kasashen musulmi ta wannan hanyar ce kawai za a iya farfado da karfin tattalin arzikinsu. Ya kara da cewa wannan zai taimaka wa kamfanonin kasashen musulmi wajen shiga cikin harkoki na kasuwannin duniya kamar yadda ya kamata domin a dama da su, ya kara da cewa da zaran an kammala gudanar da shirin za a gina babbar cibiyar wannan Hadaka ta kamfanonin kasashen musulmi a kasar Belgium.
406931