Bangaren kasa da kasa: Ofishin sheikh Hassan Saffar masanin na kasar saudiyya kuma limamin juma'a na garin Kadif ya fitar da wani bayani a jiya, da acikinsa yak e mika sakon ta'aziyya ga dukkanin duniyar musulmi dangane da asarar da aka yi ta babban malamin addinin musulunci Ayatollah Bahjat.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin interner na saffar.org cewa; Ofishin sheikh Hassan Saffar masanin na kasar saudiyya kuma limamin juma'a na garin Kadif ya fitar da wani bayani a jiya, da acikinsa yak e mika sakon ta'aziyya ga dukkanin duniyar musulmi dangane da asarar da aka yi ta babban malamin addinin musulunci Ayatollah Bahjat. Bayanin ya kara da cewa rayuwar Ayatollah bahjat rayuwa ce da ta kasance cike da ayoyi da kuma abin koyi ga dukkanin al'ummar musulmi, domin rayuwa ce ta irfani da gudun duniya da komawa zuwa ga Allah madaukakin sarki a cikin dukkanin lamurra, rayuwa ce ta koyi da manzon Allah da iyalan gidansa AS, rayuwa ce ta kamala da daukakar ruhin mutum zuwa ga babban matsayi na kusanci da ubangiji madaukakakin sarki. A daya bangaren malaman addinin musulunci na yankunan kadif sun isar da sakonnin ta'aziyya ga al'ummar musulmi dangane da wannan babban rashi.
407013