Bangaren tunani da ilimi: tarihi ya tabbatar da yadda malummai na falsafa musulmi suka yi tasiri a tunanin malumman falsafa na yahudawa>
Gulam Husein Ibrahimi Didani malamin Falsafa a jami'ar Tehran a wata hira da tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana yadda litaffai na musulmi sun kayi tasiri a tunani da nazarin malumman falsafa na yahudawa da hakan ke bayyanawa da tabbatar da karfin tunanin da nazarin malumman falsafa musulmi a tsawon tarihi. Sai dai ya yi nuni da ishara da yadda malumman falsafa na yahudawa sun canja da dama daga cikin abubuwa masu kima na ilimi da tunani a wannan fanni na falsafa da kuma lahanin da hakan ya yi wa ilimi a duniya a tsawon wannan tarihi.
405903