IQNA

Rasuwar Ayatullahi Uzma Bahajat Ya Girgiza Malumman Shi'a A Saudiya

Bangaren manema labarai: Yan Shi'a a kasar Saudiya musamman malummansu sun bayyana alhini a fili dangane da rasuwar Ayatullahi Uzma Bahajat day a rasu a cikin wannan mako.
Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta hukumar kula da ayyukan Hajji cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Hasan Saffar daya daga cikin mashahuran yan shi'a a kasar Saudiya ya bayyana cewa: Yan Shi'a da Malumman Shi'a a kasar Saudiya sun nuna bakin ciki da lahininsu na jin labarin rasuwar Ayatullahi Uzma Bahajat day a rasu yanada shekaru 96 a duniya kuma wanda ya yi fice a fanning day a shafi tsoran Allah da takawa da kuma dinbin ilimi na addini musamman Fikihu da Usul.



407355