Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Ayatollah Ozma Muhammad taki Bahjat daya ne daga cikin manyan malamai a kasar Iran, wanda aka haife shi a cikin shekara ta 1334 hijira kamariya, a wani gida na mutane masu addini da tsoron Allah a garin Komani da ke cikin Iran, ya yi karatu a hannun malamai a garin na Koman, daga nan kuma ya tafi birnin Karbala na kasar Iraki, inda ya kwashe shekaru hudu yana kwasar ilimi a hannun malamai a birnin, a lokaci guda kuma yana tarbiyantar da ruhinsa tare da yawaita ziyara a hubbaren Imam Hossain AS. Daga bisani ya koma birnin Najaf Ashraf domin ci gaba da karatu a hannun manyan malamai da ake komawa zuwa gare su da ke cikin birnin mai alfarma. Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Uzma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa Wannan babban mutum daya ne daga cikin manayan mutane, manyan malamai da ake komawa zuwa gare su, manyan muminai masu tsoron Allah, masu koyi da iyalan gidan manzon Allah, masu tsarkin zuciya da ruhi. Ayatollah bahjat ya yi rubuce-rubuce da dama a fannonin ilimin addinin musulunci.
407845