Bangaren kasa da kasa: Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta kasar Iraki ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar jiya cewa; Ayatollah Bahjat babban abin koyi net a fuskacin tsoron Allah gudun duniya mayar da lamurra ga Allah, kuma rashinsa babban rashi ne ga duniyar musulmi, rashi ne na wani babban jigo na ilimi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Brana na kasar Iraki cewa; Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta kasar Iraki ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar jiya cewa; Ayatollah Bahjat babban abin koyi net a fuskacin tsoron Allah gudun duniya mayar da lamurra ga Allah, kuma rashinsa babban rashi ne ga duniyar musulmi, rashi ne na wani babban jigo na ilimi. Bayanin ya ci gaba da a madadin dukkanin malaman addini na Hauza da ke sassa daban-daban na kasar Iraki, da alummar musulmi ta kasar, wannan cibiya tana mika sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar Iran da ma dukkanin musulmi baki daya kan wannan babban rashi da aka yi.
407588