IQNA

Ya Kamata Yammacin Turai Su Nuna Kyakkyawar Aniyarsu Dangane Da Musulunci

Bangaren kasa da kasa; Sakataren kwamitin kula da harkokin addinin musulunci na kasar Masar Muhammad Shahat Aljundi ya bayyana cewa; babbar nasarar da tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kasashen yammacin turai kan addinin musulunci zata samu, hakan ya dogara ne da nuna kyakkyawar aniya daga bangaren yammacin turai kan addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alsharq alausat cewa; Sakataren kwamitin kula da harkokin addinin musulunci na kasar Masar Muhammad Shahat Aljundi ya bayyana cewa; babbar nasarar da tattaunawa tsakanin kasashen musulmi da kasashen yammacin turai kan addinin musulunci zata samu, hakan ya dogara ne da nuna kyakkyawar aniya daga bangaren yammacin turai kan addinin musulunci. Ya ci gaba da cewa al'ummar musulmi bat a da wata baker aniya dangane da wani addini ko wata al'umma, amma kuma a kowane lokaci bat a amincewa da wulakanta tsarkakan abubuwan da ta yi imani da su. Dole ne yammacin turai su taka wa ayyukan cin zarafi kan addinin musulunci birki, idan hard a gaske yi suke yi kan tattaunawa tsakaninsu da musulmi.

407641