IQNA

Ana Zaman Makokin Rasuwar Ayatollah Bahjat A Bahrain

Bangaren kasa da kasa; Ana gudanar da zaman makoki dangane rasuwar Ayatollah Bahjat a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran kasar Bahrain cewa; Ana gudanar da zaman makoki dangane rasuwar Ayatollah Bahjat a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain. Bayanin ya ci gaba da cewa a wajen wannan zaman makoki manyan malamai na mazhabar shi'a n akasar Bahrain duk suna halartar wajen zaman makokin, a babbar husainiyar Al-sanabus da ke birnin Manama. Bayanain ya ci gaba da cewa babbar majalisar mabiya mazhabar shi'a ta kasar Bahrain ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta bayyana cewa, rashin Ayatollah Bahjat babban rashi ne ga duniyar musulmi baki daya, kuma ta mika sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar Iran da ma sauran musulmin duniya baki daya.

407765