IQNA

An Bukaci Gwamnatin Saudiyya Da Ta Kawo Karshen Kafirta Shi'a A Kasar

14:05 - May 21, 2009
Lambar Labari: 1781246
Bangaren kasa da kasa: Sama da masana dari shida daga cikin mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya ne suke fitar da wani bayani na bai daya, da ke yin Allawadai da kalaman Adil Kalbani limamin masallacin Makka da yake kafirta mabiya mazhabar shi'a, tare da neman gwamnatin kasar da ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen kawo karshen hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daga tashar gidan talabijin ta Rasid cewa; Sama da masana dari shida daga cikin mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya ne suke fitar da wani bayani na bai daya, da ke yin Allawadai da kalaman Adil Kalbani limamin masallacin Makka da yake kafirta mabiya mazhabar shi'a, tare da neman gwamnatin kasar da ta dauki dukkanin matakan da suka dace wajen kawo karshen hakan. Bayanin ya ce ya kamata ne gwamnatin kasar ta kafa wasu dokoki na hana kafirta shi'a tare da hukunta duk wanda ya yi hakan, kamar yadda bayanin ya bukaci da a hkunta Adil Kalbani bisa kalaman cin zarafi da batunci da neman kawo tashin hankali da ya yi tsakanin al'ummar musulmi.

408306


captcha