IQNA

An Fara Gudanar Da Zama Kan Harkokin Kudi A Musulunce A Bahrain

Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da zama kan harkokin kudi a musulunce a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, wanda kuma wannan shi ne karo na takwas da ake gudanar da irin wannan zama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran gna cewa; An fara gudanar da zama kan harkokin kudi a musulunce a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain, wanda kuma wannan shi ne karo na takwas da ake gudanar da irin wannan zama.Rahoton ya ci gaba da cewa taron yana samun halartar wakilan cibiyoyin kudi da bankuna daga kasashen musulmi da ma wadanda ban a musulmi ba, inda ake tattauna batutuwa da suka shafi harkokin kudi a cibiyoyin kudi da harkokin kasuwanci da bankuna na kasashen musulmi, da kum abayyana mahangarsu dangane da yadda za a kara bunkasa harkokin tattalin arziki tsakanin wadannan kamfanoni da cibiyoyi da sauran bankuna da kamfanoni na kasashen dab a na musulmi ba , amma bisa mahanga ta addinin musulunci.

408278