IQNA

An Gudanar Da Gasar Tajwidin Kur'ani Ta Mata A Palastine

16:05 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1781976
Bangaren kasa da kasa; A jiya ne aka kawo karshen gasar ka'idojin karatun kur'ani wato tajwid ta mata a Palastinu, wadda ta samu halartar daliban jami'a da na sakandare da ke garin nablus a gabar yamma da kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga gidan talabijin Palastine cewa; A jiya ne aka kawo karshen gasar ka'idojin karatun kur'ani wato tajwid ta mata a Palastinu, wadda ta samu halartar daliban jami'a da na sakandare da ke garin nablus a gabar yamma da kogin Jordan. An gudanar da wannan gasa ne a babban dakin taro na jami'ar Qods da ke birnin Nablus, shugabar kwamitin tsara gasar kur'ani ta mata a yankunan palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan ta bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce karfafa gwiwar mata musamman ma dalibai daga cikin wajen bayar da himma kan karatun kur'ani mai tsarki.

409041

captcha