IQNA

Kotun Holand Ta Sha Alwashin Hukunta Geert Wilders

16:05 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1781977
Bangaren kasa da kasa: Babbar kotun koli ta kasar Holland ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen gurfanar dad an majalisar dokoki na kasar Gerrt Wilders sakamakon ayyukan nuna tsokana da yake ci gaba da yi ga musulmi tare da cin zarafin addininsu, wanda hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa, da dokokin kasar ta Holand.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar American News cewa; Babbar kotun koli ta kasar Holland ta jaddada cewa babu gudu babu ja da baya wajen gurfanar dad an majalisar dokoki na kasar Gerrt Wilders sakamakon ayyukan nuna tsokana da yake ci gaba da yi ga musulmi tare da cin zarafin addininsu, wanda hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa, da dokokin kasar ta Holand. Babbar kotun kolin kasar ta Holand ta sanar da hakan ne jiya, bayan da Geert Wilders ta hanyar lauyoyi masu kare shi ya bukaci kotun da ta janye batun gurfanar da shi kan cin zarafin musulmi da addinin musulunci da yake yi. A cikin shekara ta 2008 ne Geert Wilders ya fitar da wani fim da a cikinsa yake wulakanta kur'ani mai tsarki, lamarin ya jawo fushin musulmi da wadanda ba ma musulmi daga sassa daban-daban na duniya.



409040
captcha