Bangaren kasa da kasa: Shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahrain Allamah Isa Qasim ya bayyana cewa kafa wannan cibiyar ilimin addinin musulunci ko kuma Hauza ta kasa da kasa a Bahrain, zai taimaka matuka wajen hada kan dukkanin masu neman ilimi na hauza a dukkanin kasashen tekun fasha.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Awal cewa; Shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahrain Allamah Isa Qasim ya bayyana cewa kafa wannan cibiyar ilimin addinin musulunci ko kuma Hauza ta kasa da kasa a Bahrain, zai taimaka matuka wajen hada kan dukkanin masu neman ilimi na hauza a dukkanin kasashen tekun fasha. Allamah Isa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain dangane da zagayowar shekarar rasuwar daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a na kasar Bahrain Sheikh Bakir Usfur. Taron dai ya samu halartar manyan malamai da kuma masana daga sassa daban-daban na kasar Bahrain. Dangane da batun kafa cibiyar ilimi ta kasa da kasa kuwa malamin ya jaddada cewa yanzu haka ana cikin gudanar da aiki kamar yadda ya kamata domin cimma wannan buri.
409080