IQNA

Qatar Za Ta Samar Da Wata Hanya Ta Nazarin Ilmomin Kur'ani

16:04 - May 23, 2009
Lambar Labari: 1781986
Bangaren kasa da kasa:Cibiyar kula da nazari da bincike kan harkokin kur'ani da ilmominsa na shirin samara da wata hanya mafi sauki wajen yin nazari kan ilmomin kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Qatar Al-raya cewa; Cibiyar kula da nazari da bincike kan harkokin kur'ani da ilmominsa na shirin samara da wata hanya mafi sauki wajen yin nazari kan ilmomin kur'ani mai tsarki. Bayanin ya ci gaba da cewa za a aiwatar da wannan shiri ne bisa hadin gwiwa tsakanin ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Qatar da kuma cibiyar kula da harkokin kur'ani ta kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan hanyar za ta taimaka ma masu gudanar da bincike kan ilmomin kur'ani, tare da sanin surori da kuma ayoyin da ke cikinsu tare da sanin dalilan safkar ayoyin ko surorin. Bayanin y ace da zaran shirin ya kammala za a sanar da shi a kafofin yada labarai ta yadda za a iya yin amfani da shi kai tsaye ta hanyar internet.

409107
captcha