Bangaren kasa da kasa: An buga tare da yada wani littafi dangane da aikin hajji a cikin kur'ani mai tsarki a birnin Katif na kasar saudiyya, tare da yin sharhi dangane da ayoyin da ke cikin kur'ani da ke bayani da faralin hajji, wanda cibiyar Nur ta dauki nauyin bugawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga tashar talabijin ta Alfajr cewa; An buga tare da yada wani littafi dangane da aikin hajji a cikin kur'ani mai tsarki a birnin Katif na kasar saudiyya, tare da yin sharhi dangane da ayoyin da ke cikin kur'ani da ke bayani da faralin hajji, wanda cibiyar Nur ta dauki nauyin bugawa. Bayanin ya ci gaba da cewa marubucin nan na kasar saudiyya mazaunin yankin Katif Hossein Abdullah Dahnim shi ne ya rubuta wannan littafi domin yin Karin haske ga mahajjata da ke safke farali ko kuma maniyyata. Marubucin ya yi kokarin bayyana ayoyin kur'ani da suka safka kan batun hajji, da kuma yadda manzon ya aikata aikin haji tare da sahabbansa, ta yadda hakan zai ma shi ne babban dalili na ma'anar ayoyin da kuma yadda ya kamata mai aikin haji ya aiwatar da su a aikace.
409122