Bayan ta nakalto daga tashar labarai ta Rasid cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: yan shi'a a Saudiya sun fitar da wani bayanida a cikinsa suke Allah wadai da abin da Adal Alkalbani limamin masallacin Haram a Makka ya yi na kafirta yan shi'a tare da bukatar hukumta wadanda ke kafirta yan shi'a. A cikin wannan bayani wadanda suka sa hannu a cikin wannan bayani sun yi mamakin yadda mahukumta suka yi gum da bakinsu bas u cewa wani abu kan wannan lamari mai hadari da zai iya kawao rarrabuwar kawuna tsakanin musulmi.
408306