Bayan ta nakalto daga shafin Internet na shura ta malumman shi'a a Bahran cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa: Ayatullahi Al'uzma Ja'afar Subhani malami a hauzar ilimi ta birnin Qum a cikin wata makala da ta yi bayani da bincike kan ismar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa a cikin kur'ani ya rubuta cewa: idan isimar Annabawan Allah abin amincewa net a hanyar hankali da zurfafa tunani to haka lamarin yake a cikin kur'ani. Ya yi ishara da aya ta 105 a cikin suratul Nisayi da ta yi bayani a fili karara kan wannan Magana mai muhimmanci a akida da rayuwa ta addini da hankali .
327010