IQNA

Katar Ta Gina Wata Otel Mai Tauraro Biyar Karkashin Tsarin Musulunci

Bangaren kasa da kasa: jami'an da ke kula da yawon shakatawa a kasar Katar sun kuduri aniyar gina wata otel mai matsayin tauraro biyar a birnin Doha babban birnin kasar karkashin zane da tsari na musulunci.
Bayan ta nakalto daga jaridar Katari ta Alwatan cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Sunya ashur shugaban bangaren zane-zane a kamfanin AJ na kasar Katar kan wannan lamari ya bayyana cewa: wannan otel za a gina ta karkashin tsari na musulunci kuma a lokutta mabambanta kuma ya ya kumshi sunna da al'adu na musulunci. Ya yi ishara da cewa: Kafin fara wannan aiki aike lokacin da dama ga masu son sanya hannayen jari kuma bayan kiyaye dokokin musulunci har ila yau akwai tsari da al'adu na musuluncin .

408470