IQNA

OIC Ta Bukaci Cikakken Goyon Bayan Kasashen Musulmi Ga Palastine

15:37 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782430
Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Ihsan Akmaluddi Auglo a wani taron manema labarai da ya gabatar a birnin Demascus na kasar Syria, ya bukaci cikakken goyon bayan kasashen musulmi ga al'ummar Palastine.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Ihsan Akmaluddi Auglo a wani taron manema labarai da ya gabatar a birnin Demascus na kasar Syria, ya bukaci cikakken goyon bayan kasashen musulmi ga al'ummar Palastine. Ya ci gaba da cewa goyon bayan da al'ummar Palastinu ke bukata daga sauran kasashen musulmi ba wai taimako ne kawai na nuna goyon baya da tausayawa ba, taimakon da suke bukata daga sauran 'yan uwansu musulmi ya hada da taimako da na tattalin arziki, goyon baya na siyasa a cikin dukkanin lamurra da suka shafi halin da yahudawan sahyuniya suka jefa ciki, da kuma batun yunkurin da yahudawan suke na mayar da birnin Qods mallakin yahudawa zalla, tare da rushe dukkanin wurare masu tsarki da ke birnin.

409521


captcha