IQNA

Obama Na Bukatar Halartar Shugabannin Kasashen Musulmi A Taron Al-kahira

15:36 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782433
Bnagaren kasa da kasa: Mujallar News week ta kasar Amurka ta habarta cewa shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya nuna matukar bukatarsa dangane da halartar shugabannin kasashen musulmi a taron birnin Alkahira wanda za a gudanar nan da 'yan kwanaki masu zuwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na tashar tashar talabijin din aljazeera cewa; Mujallar News week ta kasar Amurka ta habarta cewa shugaban kasar ta Amurka Barack Obama ya nuna matukar bukatarsa dangane da halartar shugabannin kasashen musulmi a taron birnin Alkahira wanda za a gudanar nan da 'yan kwanaki masu zuwa. Obama ya bayyana hakan ne a cikin wata zantawa da ta hada shi da wani ma'aikacin mujallar Richard Wolf, inda ya bayyana cewa a zaman da zai gudanar tare da shugabannin kasashen musulmi a birnin Alkahira na kasar Masar, zai gaya musu cewa shi yana girmama al'adu da cigaban musulunci, kuma yana fahimtar hakikanin koyarwa irin ta addinin musulunci, ya ce dole ne a karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai domin kara samun fahimtar juna.

409425


captcha