Bangaren al'adu da zamantakewa; Musulmin kasar Girka wadanda kuma sun e marassa rinjaye a kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da wulakanta kur'ani mai tsarki da wani dan sanda ya yi a birnin Athen fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reauters cewa; Musulmin kasar Girka wadanda kuma sun e marassa rinjaye a kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da wulakanta kur'ani mai tsarki da wani dan sanda ya yi a birnin Athen fadar mulkin kasar. Tun bayan faruwar lamarin daruruwan mabiya addinin musulunci da ke birnin Athen na kasar Girka sun gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da wulakanta kur'ani da wani dan sandan gwamnatin kasar ya yi. Shugaban gamayyar kungiyoyin musulmi na kasar Girka Na'im Qandur ya bayyana cewa, a ranar Laraba da ta gabata ce 'yan sanda suka kai wani samame a wani dakin cin abinci na wasu musulmi a birnin Athen, inda suka dauki wani kur'ani mallakin wani musulmi da ya zo cin abinci a wurin suka keta shi a gaban jama'a kuma suka sa kafa suka taka shi, lamarin day a harzuka mabiya addinin musulunci da ke birnin.
409512