IQNA

Ministan Harkokin Wajen Labanan Ya Halarci Zaman OIC A Demascus

15:36 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782436
Bangaren siyasa: Ministan harkokin wajen kasar Labanan Fauzi Salukh ya halarci zaman tattaunawa na ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Syria cewa; : Ministan harkokin wajen kasar Labanan Fauzi Salukh ya halarci zaman tattaunawa na ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Demascus fadar mulkin kasar Syria. Rahoton ya ci gaba da cewa a lokacin day a gabatar da jawabinsa a wajen taron ministan harkokin wajen kasar ta Labanan Fauzi Salukh ya bayyana dalla-dalla halin da ake ciki a kasar Labanan ta fuskacin siyasa, haka nan kuma ya yi bayani dangane da ayyukan liken asiri da wasu mutane kasar ta Labanan suke yi wa Isra'ila a cikin gida, tare da bayyana wa mahalarta taron irin mawuyacin halin da kasar ta samu kanta a ciki sakamakon siyasar Isra'ila ta zalunci da danniya.

409485





captcha