IQNA

Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Taimakon Da Amurka Za Ta Bai Wa Isara'ila

15:36 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782438
Bangaren siyasa da zamantakewa: Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta kasar Labanan Hizbullah, ta yi Allawadai da taimakon makudan kudi da gwamnatin Amurka za ta baiwa Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen kasar Labanan ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yammacin jiya, kungiyar gwagwarmayar musulunci ta kasar Labanan Hizbullah, ta yi Allawadai da taimakon makudan kudi da gwamnatin Amurka za ta baiwa Haramtacciyar Kasar Isra'ila. Bayanin ya ci gaba da cewa shirin da gwamnatin Obama take da shi na bayar da makudan kudi har dalar Amurka biliyan uku ga Isra'ila, babban abin takaici ne wanda kungiyar ke yin Allawadai da shi, domin kuwa a cewar bayanin za a yi amfani da wadannan kudin ne wajen kara karfafa zaluncin Isra'ila tare da ci gaba da mamaye yankunan palastinawa, da kuma rushe wurare masu tsarki da ke birnin Qods, gami da ci gaba da gina matsugunnan yahudawa 'yan kaka-gida a cikin yankunan palastinawa.

409470
captcha