IQNA

Za A Kafa Wata Cibiyar Koyar Da Ilmomin Kur'ani A Kossovo

15:35 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782439
Bangaren kasa da kasa: Za a kafa wata cibiyar koyar da ilmomin kur'ani a birnin Prishtina na jamhuriyar Kossovo, domin koyar da musulmin kasar karatun kur'ani da sauran ilmomi da suka danganci kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kwamitin kula da al'adu da harkokin ilmi na kungiyar hadin kan kasashen musulmi cewa; Za a kafa wata cibiyar koyar da ilmomin kur'ani a birnin Prishtina na jamhuriyar Kossovo, domin koyar da musulmin kasar karatun kur'ani da sauran ilmomi da suka danganci kur'ani mai tsarki, Bayanin ya ci gaba da cewa a nata bangaren kungiyar kula da harkokin ilimi na addinin musulunci ta duniya ISESCO za ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina wannan cibiya, kamar yadda hukumar kula da ayyukan alhairi ta kasar Kuwait ita ma za ta bayar da gudunmawa mai tsoka wajen gina wannan cibiya, daga bisani kuma za a fadada ayyukan kungiyar zuwa wasu kasashe da ke makwaftaka da kasar domin ilmantar da musulmi ilmomin kur'ani.

409477
captcha