Bangaren kasa da kasa: A daren yau ne gidan talabijin din ZDF na kasar Jamus zai watsa wani shiri mai suna Gabas kasar subahi, wanda aka shirya dangane da tarihin bayyana musulunci da kuma irin wahalhalun da musulmi suka sha a tarihi tun daga hannun kuraishawa har zuwa lokutan bayan bayyanar islama zuwa sauran yankuna.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Yeni Asya cewa; A daren yau ne gidan talabijin din ZDF na kasar Jamus zai watsa wani shiri mai suna Gabas kasar subahi, wanda aka shirya dangane da tarihin bayyana musulunci da kuma irin wahalhalun da musulmi suka sha a tarihi tun daga hannun kuraishawa har zuwa lokutan bayan bayyanar islama zuwa sauran yankuna. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan shiri ya kunshi fim da kuma bayanai wadanda aka harhada dangane da tarihin islama, kama tun daga jazeratul arab har zuwa birnin sarmakand, da kuma irin rawar da wannan addini ya taka wajen wayar da kan dan adam ta fuskacin ilimi da sanin rayuwa.
410099