IQNA

Tatsuniyar Holocoust Dubara Ce Ta Yahudawa Domin Mamaye Palastine

17:12 - May 25, 2009
Lambar Labari: 1782637
Bangaren kasa da kasa: Shahararren dan jaridar nan dan asalin kasar Masar kuma mazaunin kasar Norway Ahmad Rami, ya bayyana cewa tatsuniyar Holocoust wani shiryayyen makirci na yahudawan sahniya domin samun hujjar mamaye yankunan palastinawa marassa kariya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar Saudiyya cewa; Shahararren dan jaridar nan dan asalin kasar Masar kuma mazaunin kasar Norway Ahmad Rami, ya bayyana cewa tatsuniyar Holocoust wani shiryayyen makirci na yahudawan sahniya domin samun hujjar mamaye yankunan palastinawa marassa kariya. Ya ci gaba da cewa abin mamaki ne yadda a yammacin turai ake raya cewa ana kare hakkin dan adam da akidarsa, domin kuwa a kasashen turai duk wanda yaki amincewa da tatsuniyar Holocoust ko kuma ya nuna shakku kan afkuwar hakan an tanadi hukunci dauri a gidan kaso a kansa, amma har inda yau take babu wani hukunci a wata kasa ta turai da ta tanadi hukunci kan duk wani mutum da ya wulakanta addinin musulunci, maimakon haka ma sai ya zama matsayin gwamnatocin kasashen turai dangane da wulakanta addini shi ne hakan bayyana ra'ayi ne ko fadin albarkacin baki.

410063
captcha