Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar Almaktum cewa; A karon farko an bude wata cibiya da zata rika kula da harkokin rubuce-rubuce da aka yi kan addinin musulunci tare da shirya baje kolinsu a babbar cibiyar baje kolin kayyaki ta duniya da ke birnin Dubai cibiyar kasuwanci ta hadaddiyar daular larabawa. Bayanin ya ci gaba da cewa kafa wannan cibiya ya samu karbuwa a wajen marubuta da kuma masu zane-zane kan addinin musulunci. A nasa bangaren shugaban cibiyar kula da harkokin musulunci a Dubai ya bayyana cewa babbar manufar kafa wannan cibiya da za ta fara ayyukanta nan ba da jimawa shi ne, bayyana irin ci gaban da musulunci yake da shi tun zamunan da suka gabata, da kuma irin gudunmawar da musulunci ya bayar wajen ci gaban dan adam da ilimi da kyautata rayuwar zamantakewa.
409982