Bangaren kasa da kasa: Riko da kur'ani mai tsarki da hakan ya hada da hardarsa da kuma karanta shi da yin aiki da abin da ke cikinsa ya zama wajibi a cikin dukkanin sassa na rayuwa, musamman ma a duniyar da muka samu kanmu a cikinta da rayuwa cikinta ta fi mayar da hankali ga kyale-kyale baa bin da ke wajen Allah madaukakakin sarki ba.