IQNA

Za A Fara Bayar Da Horo Kan Harda Da Kuma Karatun Kur'ani A Pakistan

17:12 - May 25, 2009
Lambar Labari: 1782642
Bangaren kasa da kasa: Za a fara aiwatar da wani shiri na bayar da horo kan harda da kuma karatun kur'ani mai tsarki ga kananan yara a yankin Chakwal da ke kudancin kasar Pakistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Za a fara aiwatar da wani shiri na bayar da horo kan harda da kuma karatun kur'ani mai tsarki ga kananan yara a yankin Chakwal da ke kudancin kasar Pakistan. Rahoton ya ci gaba da cewa za a fara aiwatar da shirin a cibiyar kula da harkokin kur'ani ta Ka'im da ke yankin Chakwal na kasar Pakistan, kuma reshen jami'ar almostafa a kasar Pakistan ne zai dauki nauyin gudanar wannan shiri na bayar da horo. Yanzu haka dai akwai dalibai kimanin 70 da suka riga suka yi rijistar sunayin da za su fara samun wannan horo. Akasarin mahardata kur'ani da makaranta a kasar Pakistan a halin yanzu dai kanan yara ne.

407070

captcha