Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo ya bayyana cewa wajibi ne da yarataya kan kasashen musulmi baki daya su yi aiki kafada da kafada, domin karfafa harkokin tattalin arzikin kasashensu da kuma siyasarsu.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; : Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Akmaluddin Ihsan Auglo ya bayyana cewa wajibi ne da yarataya kan kasashen musulmi baki daya su yi aiki kafada da kafada, domin karfafa harkokin tattalin arzikin kasashensu da kuma siyasarsu. Auglou ya ci gaba da cewa hada karfi da karfe shi ne kawai mafita ga dukkanin matsaloli da kasashen musulmi suke fuskanta, domin daukar matakai na daidaiku ba zai fitar da kasashen msulmi daga matsaloli da dama da suke fuskanta ba, kama daga batutuwa na siyasa har zuwa batutuwa na harkokin tattalin arziki da zamantakewa, daga ciki kuwa har ma da matsalolin da al'ummar Palastinu ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya.
410028