Bangaren siyasa da zamantakewa: makiyan addinin musulunci na ta kokarin ganin sun rura wutar rikici tsakanin musulmi musamman sunna da shi'a.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa labarin cewa: Ayatullahi Uzma Makrimul Shirazi a wata gana day a yi da malumman addini da masu yada addinin musulunci ya yi masu bayanin cewa; makiya na kokarin ganin sun kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin musulmin duniya musamman a tsakanin Sunna da Shi'a saboda haka ana bukatar kowane musulmi ya yi takatsatsa da fahimtar wannan matsala mai girma da yadda za a warware ta.
409996