IQNA

Karfin Musulmi Na Tattare Ne Da Hadin Kai A Tsakaninsu

16:35 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783475
Bangaren kasa da kasa: Karfin al'ummar musulmi tare da komawa zuwa ga izzarsu na damfare ne da yin riko da koyarwar addinin musulunci ta hakika, tare da samun hadin kai a tsakaninsu, domin kuwa dukkanin matsalolin da musulmi suke fuskanta yanzu a duniya sun samo asali ne daga rashin hadin kai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya was cewa; Babban sakataren kungiyar kula da harkokin musulunci ta kasa da kasa Abdullah Bin Abdulmohsen Al-turki ya bayyana cewa; karfin al'ummar musulmi tare da komawa zuwa ga izzarsu na damfare ne da yin riko da koyarwar addinin musulunci ta hakika, tare da samun hadin kai a tsakaninsu, domin kuwa dukkanin matsalolin da musulmi suke fuskanta yanzu a duniya sun samo asali ne daga rashin hadin kai. Al-turki ya furta hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a birnin Demacus na kasar Syria. Ya ce duk wani batun bambancin mazhabobi warware shi mai sauki ne tsakanin musulmi matukar dai an yi niyar aiwatar da hakan.

410845
captcha