IQNA

An Kawo Karshen Gasar Karatun Kur'ani A Kasar Turkiya

16:35 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783476
Bnagaren kasa da kasa: A jiya ne aka kammala bangare na karshe a gasar karatun kur'ani da kiran salla, wadda aka gudanar a birnin Azmir na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Yeni Safak cewa; A jiya ne aka kammala bangare na karshe a gasar karatun kur'ani da kiran salla, wadda aka gudanar a birnin Azmir na kasar Turkiya. Dalibai goma sha daya ne suka samu cancantar kaiwa ga mataki na karshe a gasar, waddanda kuma dukkaninsu daliban makarantar sakandare ne. Wannan dai na daya da cikin gasar da ta samu karbuwa a wajen al'ummar kasar Turkiya, domin kuwa tun daga lokacin da aka fara gudanar da gasar, dubban mutane ne ke halartar wurin gudanar da gasar, inda aka bayyana cewa dakin gudanar da taro na birnin Azmir wanda shi ne aka gudanar da gasar a cikinsa, ya cika taf har ya bashe, yayin daruruwan mutane sukan tsaya a waje ne domin rashin samun wurin da za su zauna a ciki.

410853

captcha