IQNA

An Girmama Wasu Mahardata Kur'ani A Kasar Turkiya

16:34 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783480
Bangaren kasa da kasa: Mutane hamsin da hudu ne suka samu shedar kammala hardar kur'ani mai tsarki a garin Akhesar na nkasar Turkiya bayan sun samu cikakkaen horo na hardar kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar zaman ta kasar Turkiya cewa; Mutane hamsin da hudu ne suka samu shedar kammala hardar kur'ani mai tsarki a garin Akhesar na nkasar Turkiya bayan sun samu cikakken horo na hardar kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin wadanda suka samu wannan sheda ta kammala hardar kur'ani mai tsarki, sun hada da yara yara maza 26 da kuma 'yan mata 28, wadanda dukkaninsu ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Turkiya ce ta basu takardun shedar kammala hardar kur'ani. Dubban mutane ne dai suka halarci taron girmama wadannan dalibai a birnin Akhesar da ke kudancin kasar Turkiya. Ministan kula da harkokin addini na kasar ya tabbatar da cewa za a ci gaba da bayar da irin wannan sheda ga wadanda suka samu horo na hardar kur'ani.

410794


captcha