Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Bernama cewa; Za a kafa wata babbar cibiya domin gudanar da ayyukan kula da masallatai da ke fadin kasar Malazia. Rahoton ya ci gaba da cewa ministan kula da harkokin addinin musulunci na kasar Malazia Jamil Khair Bahrum shi ne ya bayyana hakan a wani taron kara wa juna ilimi da aka gudanar a birnin Kualalampour na kasar, inda ya bayyana cewa masallaci wuri mai matukar muhimmanci domin gudanar da ayyuka na ibada, kuma kula da shi yana da matukar muhimmanci domin karfafa gwiwar masu zuwa domin gudanar da ayyukansu na ibada musamman ma matasa wadanda ake kokarin jawo su zuwa masallaci domin su tashi da tarbiya irin ta addinin musulunci da koyarwarsa, da kuma riko da ibada, ya ce sun kuduri aniyar gudanar da ayyuka gadan-gadan domin cimma wannan buri.
410744