IQNA

ISESCO Ta Bukaci Kasashen Musulmi Da Su Taka Wa Isara'ila Birki

16:34 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783483
Bangaren kasa da kasa: Babban sakataren kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi ISESCO Abdulaziz Tuwaijari, ya bukaci kasashen musulmi da su taka gagarumar rawa wajen taka wa Isra'ila birki kan barazanar da take yi kan wurare masu tsarki dake birnin Qods mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait KUNA cewa; Babban sakataren kungiyar kula da harkokin ilimi da al'adu na kasashen musulmi ISESCO Abdulaziz Tuwaijari, ya bukaci kasashen musulmi da su taka gagarumar rawa wajen taka wa Isra'ila birki kan barazanar da take yi kan wurare masu tsarki dake birnin Qods mai alfarma. Tuwaijari ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi a birnin Demascus na kasar Syria. Ya ce wajibi ne da ya rataya kan dukkanin kasashen musulmi da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin taka wa Isra'ila birki, dangane da baranar da ta ke yi wa wurare masu tsarki, da dukkanin addinan da aka safkar daga sama ke girmamawa.

410673
captcha