IQNA

Za A Kafa Cibiyar Kula Da Nazarin Mazhabobin Musulunci

15:54 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783975
Bangaren kasa da kasa: Ministoci masu kula da harkokin addini na kasashen musulmi a karshen zamansu a birnin Jidda na kasar Saudiyya, sun fitar da wani bayani da acikinsa suka bukaci da a kafa wata cibiya ta kasa da kasa, da za ta rika hada bayanai domin samun sauki wajen yin nazari kan mazhabobin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya was cewa; Ministoci masu kula da harkokin addini na kasashen musulmi a karshen zamansu a birnin Jidda na kasar Saudiyya, sun fitar da wani bayani da acikinsa suka bukaci da a kafa wata cibiya ta kasa da kasa, da za ta rika hada bayanai domin samun sauki wajen yin nazari kan mazhabobin musulunci. A cikin bayanin sun bayyana cewa samara da irin wannan cibiya zai taimaka wajen kawo karshen rashin fahimta da ke akwai tsakanin mabiya mazhabobin musulunci, wanda wannan rashin fahimtar ce ta kai ga samun rarrabuwar kawunan musulmi a halin yanzu. Kuma hakan zai bayar da dama wajen samun masaniya kan kan dukkanin mazhabobi na musulmi ba tare da mayar da wani saniyar ware ba daga da'irar musulunci.

411381
captcha