IQNA

Ranar Daya Ga watan Rajab Rana Ce Ta Mahardata Kur'ani A Turkiya

15:53 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783977
Bnagaren kasa da kasa; Kwamitin kula hardar kur'ani a kasar Turkiya ya bayyana ranar farko ta kowane watan Rajab a matsayin ranar mahardata kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Milligazet na kasar Turkiya cewa; Kwamitin kula hardar kur'ani a kasar Turkiya ya bayyana ranar farko ta kowane watan Rajab a matsayin ranar mahardata kurni. Babban sakataren kwamitin Abdulkadir Shagolam ya bayyana cewa saboda matukar muhimmancin da ke tattare da hardar kur'ani mai tsarki, da kuma matsayin da mahardata suke da shi a cikin jama'a, wannan ya sa suka yanke shawar bayyana ranar daya ga watan kowane Rajab a matsayin rana ta mahardata kur'ani a duk inda suke a duniya ba na kasar Turkiya ba kawai. Ya ci gaba da cewa ko shakka babu hakan zai kara jawo hankula musulmi zuwa ga kur'ani da kuma bayar da muhimmanci wajen hardarsa, musamman ma matasa daga cikinsu, wadanda ake bukatar ganin sun tashi bisa tarbiya ta musulunci da koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki.


411444










captcha