IQNA

An Kawo Karshen Gasar Hardar Kur'ani A Birnin Istanbul

15:53 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783981
Bangaren kasa da kasa: An kawo karshen gasar hardar kur'ani da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya, da ta samu halartar mahardata kur'ani na birnin da kewaye gami da manyan malaman addinin musulunci da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Yeni safak cewa; An kawo karshen gasar hardar kur'ani da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya, da ta samu halartar mahardata kur'ani na birnin da kewaye gami da manyan malaman addinin musulunci da ke birnin.Rahoton ya ci gaba da cewa daga cikin wadanda suka samu halartar wajen gudanar da wannan gasa har babban malami mai bayar da fatawa na birnin Mostafa Jagrichi da kuma wasu manyan malamai. Dukkanin wadanda suka yi nasara wajen lashe gasar a bangarorin da suka kara da juna sun samu kyautuka na musamman, kamar yadda aka bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka shiga gasar baki daya.

411425
captcha